Wednesday, 25 October 2017

Karamin yaro da kanwarshi sun saci tsire ana cikin sallar Magariba

Wani karamin yaro da bai wuce shekaru goma sha uku ba da kanwarshi sun zo wucewa ta gurin wani me sayar da nama lokacin ana sallar Magariba da yaron ya duba yaga me naman baya nan kuma a iya waige-waigenshi babu me kallonshi, sai ya zari tsire suka falla da gudu shi da kanwarshi, aikuwa ashe wani daga can da yake tahowa ya gansu, aikuwa sai ya bisu mutane da suka ga haka, dama ana jira, sai aka bisu da gudu.Da yaron yaga tabbas kamasu za'ayi sai suka shige wani lungu yaba kanwar tashi tsiren ta gudu, shi kuma ya tsaya aka kamashi.

Nan fa aka fara tallabarmai keya aka kuma nemi kanwartashi sama ko kasa ba'a gantaba kuma babu tsiren a hannunshi, haka aka hada yaronnan da 'yan banga saida mahaifinshi yazo ya biya kudin tsiren sannan aka sakeshi.

Yaro yayi abinda be kamataba kuma ya kamata a mai hukunci daidai gwargwado da Nasiha.

Amma akwai dumbin darasi tattare da wannan labarin........Allah yasa mu fahimta, ya kuma shiryemu baki daya.

No comments:

Post a Comment