Wednesday, 25 October 2017

Karanta wasikar neman gafarar da Rahama Sadau ta rubutaAbin da wasikar ta kunsa
Ta rubuta cewa: "An kai shekara daya kenan tun faruwar wannan lamari, na yi iyakar kokarina don na nutsu sosai ta yadda ba za a bai wa kalamaina wata ma'ana ta daban ba kamar yadda kafofin yada labarai da wasu mutane suka dinga yi a baya."
"Ni 'yar adam ce wacce ba ta kubuta daga aikata kuskure ba, kuma ni 'ya ce wadda za a iya yi wa gyara, ina rokon abokan aikina, da mambobin kungiyar masu shirya fina-finai, da dukkan al'ummar arewacin Najeriya da ma dukkan masu kallo da su gafarce ni," in ji Rahama.

Kazalika, jarumar ta yi magana a wasu gidajen rediyo na jihar Kano, inda ta jaddada neman gafarar musamman ga Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II da kuma gwamnan jihar Dr Abdullahi Umar Ganduje.

A karshen wasikar dai Rahama ta yi alkawarin bin dokokin da kungiyar ta shimfida.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment