Monday, 30 October 2017

Kuskuren da Sa'adiya Adam tayi wajan fadar wata kalmar turanci ya jawo cece-kuce

Jarumar Fina-finan Hausa Sa'adiya Adam tayi wani gajeren bidiyo inda take gayyatar masoyanta suje gidan kallo dake Ado Bayaro Mall, Kano domin kallon wani sabon shirin fim da zai fito, a cikin wannan bidiyon Sa'adiya tayi kuskuren fadin kalmar MALL inda ta kirata da MALT, tun bayan da ta wallafa wannan bidiyon a dandalinta na sada zumunta abin ya jawo cece-kuce da zazzafar muhawara musamman tsakanin masoyanta da kuma masu ra'ayin finafinan Hausa.


Da yawa sun mata dariya bisa wannan kuskure da tayi yayin da wasu kuma sun bata uzurin cewa ai kuskurene kuma kowa, duk ilimin ka zaka iyayi, musamman ma kasancewar turanci yaren arone gurin 'yan Najeriya. 
Bidiyon da Sa'adiya tayi kuskure a ciki

Tuni Sa'adiya Adam ta janye wannan bidiyon da tayi daga dandalinta na sada zumunta saboda irin magan-ganun da akeyi akanshi, sannan ta fitar da wani gajeren bidiyon inda tayi rokon cewa dan Allah mutane su rikawa mutum uzuri idan yayi kuskure, inda tace mutum zai iya yin kuskure wajan rubutu ko kuma wajan magana, Amma tana roko a rika yiwa mutane uzuri, daga nan kuma sai ta fadi kalmar "MALL" daidai.

Bidiyon da Sa'adiya tayi gyara sannan ta roki a mata uzuri

No comments:

Post a Comment