Sunday, 29 October 2017

Kwankwaso ya sake haduwa da wasu daga cikin wadanda ya dauki nauyin karatunsu suka zama matuka jirgin sama

Alheri gadon bacci, Alheri baya faduwa kasa banza,  a kwanakin bayane tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya hadu da daya daga cikin matasan da ya dauki nayin karantunsu lokacin yana gwamna zuwa kasar Jordan inda suka koyi tukin jirgin sama a cikin wani jirgi kan hanyarshi ta zuwa Legas, labarin ya yadu da yawa akaita sawa Kwankwaso Albarka saboda wannan abin yabo da yayi. To gashi a karo na biyu Kwankwason ya sake haduwa da guda biyu daga cikin irin matasan daya dauki nauyin karatun nasu a jirgin sama inda yake kanhanyar zuwa Legas.Sanata Kwankwaso yaji dadin haduwa dasu suma sunji dadin ganinshi har suka dauki hoto tare, haka kuma kwankwaso yayi Alfahari dasu domin duk sun zama matuka jirgi a yanzu.

No comments:

Post a Comment