Tuesday, 17 October 2017

Labari me taba zuciya: Yadda harin bam ya kashe yarinya ana gobe za ta zama likita


Sa'o'i 24 gabanin Maryam Abdullahi ta kammala karatun aikin likita ne harin bam mafi muni a tarihin kasar Somaliya ya yi ajalinta.

Maryam tana daya daga cikin daruruwan mutanen da harin da aka kai birnin Mogadishu ya rutsa da su ranar Asabar.

'Yar uwar marigayiyar, Anfa'a, ta shaida wa BBC cewa lamarin ya kidimata "kwarai da gaske"."Danginmu sun girgiza sosai, musamman mahaifinmu wanda ya taho Mogadishi daga birnin Landan domin ya halarci bikin yayeta, amman maimakon hakan sai ya halarci jana'izarta."
Anfa'a ta ce ta yi magana da 'yar uwarta minti 20 kafin tashin bam din da ya jawo mummunar asarar rayuka da dukiya a Mogadishu.

"A wanna lokacin tana cikin asibitin Banadir Hospital inda take aiki. Ta gaya min tana jiran wasu fayel-fayel daga asibiti." Daga nan sai ta dauki alkawarin da Ubangiji bai ba ta ikon ciwa ba, "zan kira ki zuwa an jima," in ji marigayiyar.

Daga bbchausa.

Allah sarki kamar a zubar da hawaye, Ya Allah ka kai Rahama kabarin wannan baiwar Allah da sauran musulmi da suka rasa rayukansu a wannan hari dama dukkan musulmin da suka rigamu gidan gaskiya.

No comments:

Post a Comment