Saturday, 28 October 2017

Likitoci sun raba Tagwayen nan 'yan kasar Indiya da aka haifesu kai a hade

Yarannan 'yan kaasar Indiya da aka haifesu kawunansu a hade da labarinsu ya karade kusan ko ina, likitoci sun samu nasarar raba su cikin ikon Allah, yaran da ake kira da sunayen Jada da Kalia an bayyana cewa idan ba'ayi kokarin rabasu ba to akwai tsammanin cewa idan suka kai shekaru biyu da haihuwa a Duniya zasi iya mutuwa.Amma dayake Allahne gagara misali yake abinshi yanda yaso sai gashi ya karyata likitocin yaran sun kai har shekaru biyu da rabi da haihuwa amma basu mutuba. Yaran suna amfani da magidanar juni dayane da kuma wasu bangarori na kwakwalen su a hade yake.

Likitoci talatinne daga bangarorin Duniya daban-dabam suka hallara a Indiya tare da taimakon wasu nos-nos guda Ashirin da kuma karin wasu masu kananan ayyuka suka shafe awanni goma sha daya suna aikin raba yaran kamin su samu nasara.

An taba yin kokarin raba yaran a watan Agustan daya gabata amma ba'aci nasara ba sai yanzu.
Yanzu dai an raba yaran cikin nasara da ikon Allah, wani likita daya kware wajan yin dashen bangarorin jikin dan Adam da yake ciki likitocin da suke yiwa yaran aiki yace abu mafi wahala shine samun abinda zai rufe wawakeken ramin dake kawunan yaran bayan da aka rabasu, a yanzu dai yace wata 'yar balan-balance da akayi amfani da ita a aikin da aka musu na farko take rufe da kawunan yaran, yanzu kuma aiki ya rage ga likitocu masu da she a jikin dan Adam su samo abinda zai rufe kawunan yaran.
Tsarki ya tabbata ga Allah ubangijin talikai, Allah ka karawa Annabi salati da Alayensa.

No comments:

Post a Comment