Wednesday, 18 October 2017

Matan Gwamnonin Arewa sunyi taro a jihar Bauchi

Matan gwamnonin  jihohin Arewa sunyi taro a dakin taro dake gandun dajin Yankari na Jihar Bauchi, taron nasu wanda ya samu halartar gwamnan jihar Muhammad Abdullahi Abubakar wanda daga baya kuma suka shiga tattaunawa a tsakaninsu, sun nada matar gwamnan jihar Bauchin Hajiya Hadiza Abubakar a matsayin sabuwar shugabar kungiyar matan gwamnonin Arewar,  sannan kuma sun tabo batutuwan magance matsalar shaye-shaye da rigakafin cututtuka.Bayan taron nasu sun zagaya cikin dajin na Yankari sannan akayi wata liyafar cin abinci ta musamman.
Haka kuma matan gwamnonin sun ziyarci wata makarantar yara a jihar Bauchin dake bukatar kulawa ta musamman sun basu kayan agaji da suka hada da abinci da da sauransu.
Matan gwamnonin sun kuma kaiwa sarkin Bauchi Dr. Rilwanu Adamu ziyara inda suka nemi basu hadin kai akan ayyukan Alherin da suka sa a gaba.No comments:

Post a Comment