Tuesday, 10 October 2017

Matasan jihar Kebbi sunyi abin yabo: Sun daina amsa kiran 'yan siyasa saboda sun samu aikinyi


Wani labari me ban sha'awa da birgewa game da wasu matasan jihar Kebbi daya faru ya dauki hankulan mutane musamman a shafukan sada zumunta da muhawara, Gwamna Atiku Bagudu ya bayar da labarin yanda ya gayyaci wasu matasa zuwa fadarshi domin ya gana dasu amma yace abin mamaki matasan sai suka aikamishi da takarda cewa bazasu samu zuwa a ranar daya bukaci sujeba saboda zasuyi girbin shinkafa da alkamarsu, saidai ya saka musu wata ranar, gwamnan ya bukaci matasan da su zabi ranar da sukaga tayi musu, gwamnan yace wannan abu ya matukar birgeshi kuma ya bashi mamaki saboda ya saba idan ya gayyaci matasa zuwa gidan gwamnati suna rawar jiki zasuso da kwadayin me zasu samu na sakawa Aljihunansu.


Bayan jin wannan labari ministan harkokin noma Audu Ogbe ya gayawa Gwamna Bagudu cewa to lallai idan haka na faruwa wataran 'yan siyasa zasu kira gangamin kamfe amma matasa su gayamusu suna da aikinyi, ya kara da cewa watakila saidai 'yan siyasar su rika bin talakawa/masu zabe a gonakinsu suna neman su zabesu.


No comments:

Post a Comment