Monday, 23 October 2017

"Maza ku ajiye lefenku muma mu ajiye kayan daki da gara">>inji wata budurwa

Taufa ana wata ga wata, da alama wannan budurwar me suna Fadila Abubakar Alkali ta hasala da maganar da wasu samari keyi cewa a daina yin Lefe saboda yana sasu kashe kudi da yawa, wasu ma na fadin cewa Lefenne ya hanasu yin Aure, fadila tace, kamar yanda ake iya gani a wannan hoton na sama, maza su ajiye lefensu suma(mata) su ajiye kayan daki(Gado katifa kujeru kayan girki dadai sauransu) da gara kowa ya huta.

Ga abinda ta rubuta kamar yanda yake a cikin hotonnan na sama.

 "Nifa yadda maza suka tsani lefe abun na ban mamaki....ku aje lefenku muma mu aje kayan daki da gara....wallahi kowa ya huta".

Wannan batu na Fadila ya dauki hankulan mutane inda wasu sukace aje a hakan a kawo katifa kawai da kayan girki wasu kuma cewa sukayi idan akayi haka auren bazaiyi dadiba.

No comments:

Post a Comment