Tuesday, 3 October 2017

Meyasa ba'a kira mutumin daya kashe mutane a kasar Amurka da sunan dan ta'addaba?

Wani mutum farar fata da aka samu yayi harbe-harbe da bindiga a wani gidan rawa dake kasar Amurka wanda yayi sanadiyyar kashe mutane hamsin da takwas sannan wasu kusan dari biyar suka jikkata wanda akace a tarihin harbe-harben bindigar kasar Amurka da ake samu wannan shine yafi muni ya jawo cece-kuce a ciki da wajen kasar Amurkar, daya daga cikin batun daya fi samun magan-ganu shine kin bayyana mutumin da sunan dan ta'adda da kasar Amurkar tayi saidai kiranshi akayi da wai maharbi/ ko kuma dan bindiga.Mutumin me suna Stephen Paddock ya harbe kanshi bayan daya gama kashe mutane iya son ranshi, mutane da dama na ganin cewa saboda mutumin farar fatane kuma ba musulmi bane shiyasa aka ki cewa dan ta'addane ko kuma wannan harin daya kai na ta'addancine wato sudai Amurka fassararsu ga dan ta'adda tana aiki akan musulmaine kawai.

Wannan ya harzuka mutane da yawa inda akayi ta rubuce-rubuce a shafukan sada zumunta da muhawara sannan wasu sukayi ta sharhi a gidajen talabijin dana jaridu kuma ciki harda Amurkawan.
Allah shi kyauta ya kuma kara daukaka musulunci da musulmi koda makiyan basa so, sannan yayi mana maganin masu amfani da sunan musulunci suna aikata ayyukan assha.

No comments:

Post a Comment