Tuesday, 17 October 2017

Meyasa Duniya tayi shiru akan mummunan harin da aka kaiwa kasar Somalia?

A yayinda kasar Somalia ke cikin tashin hankali da jin jikin mummunan harin da aka kaimata wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane kusan dari uku Duniya tayi kamar bata san abinda ya faruba, kasashen Duniya da masu bayar da agaji na Duniya kusan daya-dayane suka yi magana akan wannan harin, ya zuwa yanzu dai kasar Turkiyyace kadai ta kaiwa kasar Somalia taimako na zahiri inda ta aikawa somaliyar jirgin yaki cike da kayan agaji sannan zata dauki wasu daga cikin wadanda harin ya jiwa rauni zuwa kasar tata domin basu magunguna kyauta.Haka kuma daga kasashen yamma kasar Faransace kawai ta nuna alhinin wannan mummunan harin, an kashe fitilun dake haska wannan zungureren karfen na birnin Paris me suna Eiffel Tower na dan wani lokaci kamar yanda ta saba yi idan wani abu ya faru na tashin hankali a Duniya.

Bayan wadannan babu wata kasa data nuna rashin jin dadin abinda ya farun a kasar Somalia kuma abin mamaki ciki harda kasashenmu na Afrika, yanzu hakadai kamar yanda rahotanni ke nunawa kasar tana bukatar akajin jini domin kula da marasa lafiya da kuma kayan aikin da za'a cire kurabazan gine-ginen da suka rufta domin gano sairan mutanen da suka bace.

Wannan yasa wasu mutane har sun fara tayar da wannan magana a dandalin sada zumunta faban-daban inda ake cewa yanzu da a Amurkane ko kuma wata kasar turawa da tuni Duniya ta dauka anata aika jaje, koda kuwa harin baikai munin hakaba.

Allah shi kyauta.

No comments:

Post a Comment