Thursday, 26 October 2017

Mutum-mutumi ta farko a Duniya da ta samu shedar zama 'yar kasa

An samu mutum-mutumi na farko da aka baiwa shaidar zama dan kasa a Duniya, Mutum mutumin wanda ake kira da suna Sophia ta samu zama 'yar kasar Saudiyya bayan da ta shahara wajan iya magana da mutane da amsa tambabyoyi da ake yi mata, daga cikin mutanen da Sophia ta yi magana da su akwai mataimakiyar sakataren majalisar dinkin Duniya kuma 'yar Najeriyar nan Amina Muhammad da kuma me baiwa shugaban kasa shawara ta fannin kafafen watsa labarai na zamani, Bashir Ahmad.Anawa Sophia kallon wani gagarumin cigaba ta fannin kirkire-kirkiren zamani da akeyi wajan kawo wa al'umma saukin rayuwa, kuma rahotanni sun nuna cewa nan ba da dadewa ba za ta samu abokai irinta watau mutum-mutumai. Wadanda suka kirkirota sunce idan aka sami ire-iren ta da yawa, nan gaba zasu rika taimakawa wajan gudanar da ayyuka a guraren taro da kuma gidan kula da tsoffi.
Sophia ta bayyana jin dadinta ga samun shedar zama 'yar kasar Saubiyya.

Hmmmm....Duniya inda ranka zakaji ka gani.

No comments:

Post a Comment