Saturday, 14 October 2017

Nagodewa Allah da hasken musulunci, shekaru hudu da suka gabata na yanke shawara mafi muhimmaci a rayuwata>>Inji wata baiwar Allah da take murnar cika shekaru hudu da musulunta

Wannan baiwar Allahn dake amfani da sunan Ayush Hadeya a dandalin sada zumunta da muhawara na shafin Twitter tayi murnar cika shekaru hudu da musulunta, tace shekaru hudu da suka gabata ta yanke shawara mafi muhimmanci a rayuwarta watau shawarar shiga addinin musulunci, ta kara da cewa ta godewa Allah da kasancewarta musulma, wannan bayani nata ya birge mutane sosai yanda akayita nuna sha'awarshi da yimata addu'ar fatan alheri.Munamata fatan alheri da kuma fatan Allah ya karamata fahimtar addinin musulunci.No comments:

Post a Comment