Saturday, 7 October 2017

Najeriya ta samu zuwa buga gasar cin kofin Duniya da za'ayi a kasar Rasha shekarar 2018Najeriya ta samu zuwa ne bayan ta doke Zambiya da ci 1-0 a wasan da suka fafata a Uyo ranar Asabar.

Sakamakon wasan ya sa makin Najeriya a teburin ajin B na kasashen da ke neman zuwa gasar cin kofin duniya daga Nahiyar Afirka ya zama 13, yayin da Zambiya ta ke da maki 7.Ko da yake akwai wasanni biyu da kungiyoyin biyu za su buga, nasarar Najeriya a teburin ba za ta sauya ba.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment