Friday, 13 October 2017

Nazir Ahmad, Sarkin Waka ya kare Umma Shehu akan tambayar da Momo yayimata

Fitaccen mawakin Hausarnan Nazir Ahmad wanda ake kira da Sarkin Waka ya fito a dandalinshi na sada zumunta da muhawara ya kare jarumar fim din Hausarnan da Aminu Sharif Momo ya yiwa tambayar cewa wacece ta shayar da Annabi(S.A.W) a hirar da yayi da ita a tashar Arewa24 amma bata bayar da amsaba, Nazir ya jawo hankali akan cewa ya kamata mutane su rika binciken abu kamin suyi wani kalami akai, ya kara da cewa mafi yawanci ba'aga hirar dukaba, kuma mafi yawanci masu zakewa akan wannan batu suma basu san amsar tambayar da akawa Umma Shehun ba.Nazir ya kara da cewa shifa bahaushe gani yake addini nashine kawai, amma ba haka abin yakeba, kuma ya saka hoton bidiyon hirar da Aminu Sharif Momo yayi da Umma Shehun amma ba daga inda yawancin mutane suka ganiba watau daidai inda Momo yake tambayarta wa ta shayar da Annabiba, a a ya saka hirarne daidai inda Umma take zano irin litattafan da ake musu a makarantar Isilamiyya wanda Nazir yace yaya za'ace wadda tasan wadannan litattafai batasan amsar wacece ta shayar da Annabiba, to amma saboda irin yanda muhawara tayi zafi akan wannan hoton bidiyo sai Nazir ya cireshi daga dandalinshi.

Gadai abinda wasu suka bayyana akan kariyar da Nazir ya yiwa Umma Shehun.
No comments:

Post a Comment