Friday, 27 October 2017

"Rahama Sadau ce da kanta ta tuba kuma ta nemi in mata jagora ta nemi afuwa">>Ali Nuhu

A wata hira da yayi da mujallar fim, fitaccen jarumin finafinan Hausa Ali Nuhu(Sarki) ya karyata rade-radin da akeyi cewa wai shine ke ta faman ganin an yafewa Rahama Sadau lefin da tayi bawai jarumar bace da kanta ta tubaba, Ali Nuhu yace Rahamar ce ta kanta ta sameshi ta nemi ya mata jagora zuwa gurin shuwagabannin kungiyar domin ta nemi afuwa, shiyasa ya dauketa zuwa ofis-ofis dan ganin an yafe mata ta dawo taci gaba da harkar fim din Hausa.Ali ya kara da cewa yana ga dalilin da ya sa Rahama bata nemi afuwa tun a farkon abin da ya faruba ta koma gefene kowa ya huce, watakila da tayi magana a wancan lokacin babu wanda zai saurareta kuma koda dankane idan yayi lefi za kaga yana labe-labe yana jin tsoron shigowa gida dan kar a dakeshi.

Ya kara da cewa shi yana ganin a yafewa Rahama saboda idan danka yayi laifi kamata yayi ka kirashi ka ja mai kunne ka kuma mai hukunci domin idan ya shiga Duniya duk abinda yaje ya aikata ba za'a canja mishi suna ba kai ne dai za'a rika da babanshi.

Ali yace yana ganin Rahama Sadau ba za ta sake aikata irin laifin da ta aikata a bayaba saboda a wancan lokacin akwai kuruciya ga kuma daukaka to ya kamata a rikawa jarumai uzuri da kuma kula dasu dan ganin basuje sun aikata wani abu da bai daceba, yace amma mutum yana girmane hankali yana kara shigarshi shiyasa a yanzu yake tunanin ba zat ta sake aikata makamancin wancan laifin ba idan an yafe mata.

No comments:

Post a Comment