Thursday, 19 October 2017

Rahama Sadau lokacin tana rawar Indiyawa: ta samu daukaka cikin kankanin lokaci

Rayuwa kome ka saka a gaba da gaskiya da kuma taimakon Allah zaka iya kaiwa inda baka tsammani, a wannan hoton fitacciyar jarumar finafinan Hausa ce wato Rahama Sadau lokacin bata zama 'yar fim ba tana rawar indiyawa. A yau gashi a cikin shekaru Hudu kacal da fara yin finafinan Hausa duk Duniya ta santa, taje kasashen Turawa dana Amurka, ta samu kyautuka da yawa, ta hadu da babban mawakin kasar Amurka, Akon, yanzu haka kuma tana jan zarenta a fannin finafinan kudancin kasarnan.Rahama Sadau dai takan fadi cewa tauraruwar finafinan kasar Indiya, Priyanka Chopra ce gwanarta kuma tana so ta taka rawa irin tata, hakan yasa wasu ke kiranta da Priyankar Najeriya, kuma za'a iya cewa a yanzu ta samu daukakar da take nema anan cikin gida Najeriya, harma da wasu sassa na kasashen waje.

Ga dukkan alamu burin Rahama nan gaba(ta fannin sana'a) shine ta hadu da Priyanka Chopra, ta fara fitowa a finafinan Indiya da na Amurka gadan-gadan, saidai wasu alamu na nuna cewa Rahamar tana soyayya da wani wanda bata bayyawa Duniya ko wanene ba. Kuma kamar yanda ta taba bayyanawa a baya kwanannan zatayi Aure. Shin Auren zai barta ta cigaba da neman cika wadannan burikan nata, ko kuwa idan tayi Aure zata hakura da sana'ar fim?

Idan lokaci yayi, 'yar manuniya zata nuna

No comments:

Post a Comment