Wednesday, 11 October 2017

Rahama Sadau ta roki jarumin finafinan kasar Indiya Hrithik Roshan da yazo ya aureta(tana sonshi)

A yayin da al'adun nahiyar Afrika da Najeriya, musamman kasar Hausa wasu ke ganin zubar da Ajine mace ta fara furtawa namiji cewa tana sonshi, yanzu zamani yazo da wasu ke ganin an waye yin hakan ba abin damuwa bane, fitacciyar jarumar finafinan Hausa da aka kora take kuma taka rawar gani a finafinan kudu wato Rahama Sadau ta fito ta bayyana soyayyarta ga fitaccen jarumin finafinan kasar Indiya me suna Hrithik Roshan.Rahama ta bayyana hakanne kwanannan a dandalinta na sada zumunta da muhawara na shafin Twitter inda tace "Mutumin kirki da bashi da girman kai, Dan Allah ka aureni Hirithik Roshan"

Lallai wannan jarumi yana da farin jini gurin mata sosai domin yanzu haka acan kasar Indiyar yana cikin wata badakalar soyayya da wata abokiyar aikinshi me suna Kangana Ranaut tayi ikirarin cewa tayi dashi amma shi kuma ya karyata hakan.

Ba wannan ne karin farko da Rahama take bayyana soyayya ga fitattun mutanen Duniyaba, saidai wannan karin shine ta fito kiri-kiri ta bayyana a rubuce abinda take nufi, amma a baya-bayannan Rahamar ta saka hoton fitaccen dan wasan kasar Brasil dinnan da yafi kowane dan wasan kwallo tsada a Duniya wato Neymar da kuma alamar zuciya a dandalinta na shafin sada zumunta da muhawara wanda mutane da yawa suka yiwa fassarar cewa ta nuna tana sonshine.

Abinda zamu jira muji shine ko Hrithik zai amsa wannan tukwici da Rahama tayi mishi?

No comments:

Post a Comment