Thursday, 19 October 2017

Rahama Sadau ta samu shiga cikin wadanda zasu iya lashe kyautar karramawa a finafinan kudu

Watakila Rahama sadau ta kara darawa kwanannan domin kuwa an sakata a cikin wadanda zasu iya lashe wata kyautar da ake baiwa 'yan fim din kudancin kasarnan me suna Tusha Awards, sunan Rahamar ya fitone a cikin sunayen mata biyar da zasu iya lashe kyautar wadda tafi iya taka rawar matashiya a fim.Idan dai Rahama taci wannan gasa to karo na biyu kenan a wannan shekarar ta samu kyautuka daga yankin kudu a finafinan kudancin da take yi, idan aka hada da kyautar karramawa ta BON.

No comments:

Post a Comment