Sunday, 15 October 2017

"Rashin aikinyi da yawa mutane yawa shiyasa karamin abu sai ya zama abin magana, masu tsoron Allahn karyawa kawai daku">>Nafisa Abdullahi

Taufa da alama irin cece-kucen da akayi ko kuma ake cikinyi da wasu fitattun mutane musamman jaruman finafinan Hausa ya zagayo kan jaruma Nafisa Abdullahi, domin kuwa a wani rubutu da tayi a dandalinta na sada zumunta ta caccaki 'yan Najeriya akan tsoma baki da sukeyi a harkokin rayuwar wasu mutane, Nafisardai ta fara da cewane "Mafi yawancin mutane basu da aikinyi shiyasa duk wani kankanin abu daya faru sai ya zamarmusu abin magana". Ta kara da cewa "na rantse(wallahi), na sake da lamarinmu 'yan Najeriya. Tarin masu nuna tsoron Allahn karya(kawai daku)"."Nan gaba ce maka za'ayi ga yanda zuciyarka ya kamata ta rika bugawa. Gara dai ku rika maida hankali akan matsalolinku/laifukanku da kuma neman hanyar mangancesu ku daina yi kamar wai ku ma'asumaine".

Kwanannan dai Hadiza Gabon ta mayarwa da wani zazzafan martani a dandalinta na sada zumunta da Muhawara bayan daya bata shawarar cewa tayi Aure.

Haka kuma yanzu haka ana cikin cece-kuce akan wata hira da Aminu Sharif Momo yayi da jaruma Umma Shehu a gidan talabijin na Arewa24 inda ya tambayeta sunan wadda ta sahayar da Annabi(S.A.W) bayan rasuwar mahaifiyarshi amma bata bayar da amsaba sanadiyyar haka mutane da yawa suka rika kiranta Jahila wasu ma suka rika yiwa duk matan finafinan Hausar kudin goro.

Ga dukka  alamu irin wadancan abubuwa da suka farune suka tunzura Nafisa yin wannan rubutu, sai muce Allah shi kyauta.

No comments:

Post a Comment