Sunday, 22 October 2017

"Rubutun da mutum keyi da hotunan da yake sakawa a dandalinshi na sada zumunta ke nuna irin tarbiyyarshi">>Tijjani Asase

Fitaccen jarumin finafinan Hausa Tijjani Asase yayi wani kira ga mutane masu amfani da shafukan sada zumunta da muhawara na zamani me amfani, Tijjani yace ya kamata mutane su rika kula da abubuwan da suke rubutawa a dandalinsu na sadz zumunta da kuma irin hotunan da suke sakawa domin ta hakane ake gane tarbiyyar mutum kuma mutum yayi tunani idan ya mutu mutane suka duba rubuce-rubucenshi da hotunan daya saka addu'a zasumai ko kiwa  tsinuwa?Gadai abinda Tijjani ya rubuta kamar haka:

"Salam barkanmu da safiya hakika wannan dandali wurine da zaka batawa wani kafarantawa Wani kuma kaima Wani ya batama Wani kuma ya tallata hajarsa Wani kuma kansa yake talla amman ina son kasani sumutane suna gane tarbiyar kane daga zancanka da hotinan da kake sawa da haka ake gane kai wanene yadan uwana zaka iya mutuwa kuma mutane subude fejinka addu'a zasuma ko tsinuwa?"

No comments:

Post a Comment