Thursday, 26 October 2017

Rukayya Dawayya ta nuna goyon bayan a dawo da Rahama Sadau ta cigaba da yin fim din Hausa

Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa, Rukayya Dawayya ta bayyana goyon bayanta akan cewa a dawo da shahararriyar korarriyar jarumar fina-finan Hausa Rahama Sadau masana'antar fim din Hausa ta cigaba da yin fim, a wani ra'ayi data bayyana akan labarin takardar da Rahamar ta rubuta ta neman afuwa daga masu kula da harkar fim, Rukayya ta bayyana cewa "Mu dama bata mana komai ba. Dan babu wanda baya laifi saidai na wani yafi na wani, wani aga nashi a fili wani kuma a boye.Jiya ne dai Rahamar ta nemi afuwar rungumar da ta yiwa mawaki Classiq a wata waka da suka fito tare bayan kusan shekara guda da korarta daga masana'antar Fina-finan Hausa.

No comments:

Post a Comment