Monday, 9 October 2017

Sabulun 'kara fari' ya janyo dambarwa

Dove
Kamfanin Dove ya nemi afuwa bayan ya fitar da wani jerin hotunan "nuna wariya" wadanda aka ga wata bakar fata ta rikide ta zama fara sol bayan ta yi amfani da sabulunsu.
Tallar sabulun a shafin Facebook ya nuna hotu uku, inda wata bakar fata ta kwabe rigarta kuma sai ta rikide ta zama baturiya farar fata.
Yayin da hoto na uku ya nuna farar fata ta rikide ta koma Balarabiya.
A cikin wani sakon Twitter kamfanin Dove ya ce: "Mun yi matukar nadama kan zafin da hakan ya janyo."


A yanzu dai an cire bidiyon wannan talla a shafin Facebook, ko da yake, wata Ba'amurkiya mai tallan kwalliya Nay the mua ta ce ta ga hotunan sun ci gaba da bayyana a shafinta kuma har ma ta tura wa masu bibiyarta.
"Kawai ina bibbincika shafina na Facebook kuma ga tallar kamfanin #dove da ya bayyana.... shi ne abin da nake kallo ma," ta rubuta a kasan hotonta.
Dove
Al'amarin dai ya janyo dumbin muhawara a shafukan sada zumunta, inda wasu mutane ke zargin kamfanin Dove da wariyar launin fata da kuma kumbiya-kumbiya.
Wasu da ke sharhi a kasan bayanin da Nay ta wallafa sun yi saurin cewa suna jin kamfanin na son ya ce duk jinsin al'umma na iya amfani da sabulun ne.
Dove
Wata mai amfani da Facebook ta ce: "Tabbas mace ta ukun ba farar fata ba ce, kuma gaskiya wannan mummunan sako ne batun cewa kowa ma zai iya amfani da shi."
Ko a shekara ta 2011, an zargi kamfanin Dove da nuna wariya ta hanyar amfani da hotunan da ga alama na wasu mata ne guda uku, inda aka nuna cewa sakamakon amfani da sabulun kamfanin shi ne hoton macen da ta fi kowaccensu haske.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment