Tuesday, 10 October 2017

Saka riga me dauke da hoton tsohon shugaban kasa jeneral Sani Abaca yasa da jaa hankulan mutane

Wannan baiwar Allahn ta dauki hankulan mutane a dandalin sada zumunta na Twitter bayan data saka wannan rigar me dauke da hoton tsohon shugaban kasa marigayi Janaral Sani Abacha,  da alama kamar zuwa tayi aka mata zanen fuskar tsohon shugaban kasar, wasu na ganin cewa tayi hakanne dan nuna soyayya a gareshi wasu kuma na ganin tayi hakanne kawai dan tayi kwalliya ko kuma ta jaa hankulan mutane zuwa gareta.Wasu dai sun rika binciko bayanai akan marigayin da kuma bayyana cewa basuga abin birgewa da zaisa su saka riga me dauke da hotonshiba haka kuma wasu sun yaba suna kuma nuna sha'awar suma wata rana zasu iyayin koyi da wannan mata.

No comments:

Post a Comment