Thursday, 12 October 2017

Sharhi akan batun bidiyon hirar Umma Shehu da Aminu sharif Momo

Dandalin Kannywood: Jaruma Umma Shehu ta kunyata a idon duniya
Bayan da wani gajeren hoton bidiyo da Fitaccen jarumin finafinan Hausa kuma me gabatar da shirye-shirye a gidan talabijin na Arewa24 Aminu Sharif momo yayi hira da jaruma Umma shehu ya watsu a shafukan sada zumunta da muhawara inda a ciki Aminu ya tambayi Umma wadda ta shayar da Annabi(S.A.W) amma Umma bata bayar da amsaba, hakan ya jawo cece-kuce sosai yayinda wasu suka bayyana cewa Aminun yaci mutuncin Ummane domin tambayar da yayi ba muhallinta bane wasu kuma sun bayyana cewa itama ta kwafsa domin ya kamata ace ta bayar da amsar tambayar.


Wannan  rubutun na kasa sharhin wata baiwar Allahne me cike da hikima da kuma jan hankali akan wannan batu:

"Ya dai kamata gaba 1 kusan me kuke ci don irin wannan ba wai be yi dai dai bane a'a abinda ba hurumin sa ba bai kamata ace an maka makashi ba zato ba, ko mutun ya sani zai iya kufce masa sbd yazo masa a bazata badon ina kare ta ba a'a ina yi ne sbd a fahimci kure a gyara. A kalla duniya bazata kalleta ita kadai ba ku duka masu sana'ar za'a kalla kuma ai muku kudin goro. Ina fatan baka manta da annobar data ta6a barko muku tayi barazanar rusa ku wanda har yau baku koma dai dai ba, kuma duk irin wadannan abubuwa da ba'a daukarsu abu suke zama abu yakamata a gyara ko don a gudun tare a tsira tare. Kuma wannan ai nakasu ga wadanda sukasan aiki, idan ka gayyaci mutum irin wannan ya dace ka bashi haske akan abinda zaku tauna don yaje yayi binkice ya shirya kafin zuwan lkc. Bana manta lkcn da gidan wata talabijin ta gayyaci daliban makarantar dana ke sai da suka bada haske kan tambayoyin da za'a yiwa yara kuma abin yayi gwanin shaawa daya gidan talabijin da suka da da bamu gayyata da suka bada a haske akan abinda zaayi aka bawa yara horaswa akai daka je sai suka canja kuma yara basu sani ba, ba malaman kadai ba su kansu gidan TVn sun ji kunya.shi kure mutum ba dadi gaskiya. Kalubale gareku baki1 me karancin ilmi yakamata yasan me yake ciki yayi zuciya ya nemi ilmi ta kowane fanni ba don komai ba ko don bawa mahassada, makiya, yan bani na iya da yan gaja ni kunya....... Ba wanda aka halitta da iyawa amma idan kayi kokari ka iya ka kere sa'a. Taku ce ta fits fili yanzu haka akwai da yawa wanda basu San amsar tambayar ba amma suna ta zakewa da surutu da magana. Allah ya fishshemu aikin dana sani."

Amin.

No comments:

Post a Comment