Friday, 13 October 2017

Shugaba bankin Duniya ya ce shugaba Buhari ya basu umarnin maida hankali a Arewa wajan ayyukan cigaba: Hakan ya jawo cece-kuce

Shugaban bankin Duniya Jim Yung Kim ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya basu umarnin cewa su mayar da hankali wajan yin ayyukan cigaba a yankin Arewa, shugaban bankin yace kuma sunyi ko kuma suna kanyin hakan amma ya kara da cewa gaskiya yin aiki a Arewa akwai wahala, wannan magana da shugaban bankin Duniyar yayi ta jawo cece-kuce a cikin kasaranan inda wasu suka rika bayyana shugaba Buharin a matsayin shugaban da bashi da adalci, me kishin yankinshi kawai.
Wasu kuwa sun rika bashi uzurin cewa an bar yankin Arewa a baya sosai wajan cigaba idan aka kwatanta da yank8n kudu, haka kuma rikicin Boko Haram ya kara nutsar da yankin cikin halin koma baya wajan cigaban zamani.

Munawa shugaba Buhari fatan alheri, Allah ya taimakeshi akan ayyukan alheri daya saka a gaba.

No comments:

Post a Comment