Monday, 30 October 2017

Shugaba Buhari ya gana da Bukola Saraki, Yakubu Dogara, Bola Tinubu, Oyegun da Abdulaziz Yari a fadarshi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da jigo a jam'iyyar APC Bola Ahmad Tinubu a fadarshi dake Abuja, bayan ganawar tasu Tinubu yayi magana da manema labarai inda yace sun tattauna da shugaban kasar ne akan batutuwan da suka shafi cigaban kasa kuma yaji dadin hakan.Dangane da rashin ganinshi da ba'ayi a fadar shugaban kasar, Tinubu yace sunyi kokarin kafa gwamnati kuma suna da tabbacin shugaban kasa zaiyi abinda ya kamata domin sun san ko shi wanene, saboda haka ba wai sai sunyi ta zuwa suna bibiyar abubuwan dake faruwa ba.
Tinubu ya kara da cewa maganar cewa wai an mayar dashi gebe ko kuma sun samu matsalar dangantaka da shugaba Buhari wannan ba gaskiya bane.
Haka kuma shugaba Buharin ya gana da shugaban jam'iyyar ta APC, Oyegun da shuwagabannin majalisun tarayya, Bukola Saraji da Yakubu Dogara da kuma gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari.


No comments:

Post a Comment