Saturday, 21 October 2017

Shugaba Buhari ya gana da shugaba Alpha Conde na Guinea da firaiministan Pakistan Shahid Abbasi a Kasar Turkiyya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da Firaiministan kasar Pakistan Shahid Khaqan Abbasi a kasar Turkiyya inda suka hadu wajan taron kasashe takwas masu tasowa, shugaba Buhari ya kuma gana da shugaban kasar Guinea Alpha Conde.A ganawarshi da Alpha Conde shugaba Buhari ya bayyana cewa dolene idan kasashen Afrika naso su samu cigaba ta fannin tattalin arziki da tsaro su dukufa wajan samawa kawunansu hanyar warware matsalolinsu da kansu ba tare da sa hannun kasashen ketare ba.No comments:

Post a Comment