Friday, 13 October 2017

Shugaba Buhari ya gana da shuwagabannin yankin Inyamurai

A yaune shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da shuwagabannin yankin kabilar Ibo, shugaban ya bayyana musu irin muhimmancin daya baiwa yankinsu inda yace ya bayar da mukamin ministoci daga yankin sannan kuma yana kokarin ganin ya kawo ayyukan cigaba da suka hada da gina tituna da gadar Second Niger da kuma gina titunan jirgin kasa.Shugaban ya kara da cewa yana kokarin ganin gwamnatinshi bata bar wani yanki a bayaba wajan yi mishi ayyukan raya kasa da cigababa.No comments:

Post a Comment