Tuesday, 24 October 2017

Shugaba Buhari ya isa kasar Nijar dan halartar taron kungiyar kasashen yammacin Afrika


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa birni Niamey na kasar Nijar a yau inda zai halarci taron kungiyar kasashen yammacin Afrika ECOWAS a takaice, daya daga cikin muhimman batutuwan da za'a tattauna a wannan taro shine samar da takar dar kudin bai daya da kasashen dake cikin kungiyar zasu rika amfani dasu.

Ministar kudi Mrs. Kemi Adeosun da gwamnan babban bankin Najeriya CBN a takaice wato Mr. Godwi Emefiele ne suka yiwa shugaba Buharin rakiya kuma ana saran idan Allah ya yarda bayan taron shugaba Buhari da tawagarshi zasu dawo gida Najeriya. 

No comments:

Post a Comment