Monday, 30 October 2017

Shugaba Buhari ya nada sabon sakataren gwamnatiA ranar Litinin ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada sabon sakataren gwamnatin kasar, bayan da ya kori Mista Babachir Lawal bisa zargin cin hanci da rashawa.
Wane ne Boss Gida Mustapha?

Mr Boss Gida Mustapha lauya ne, dan siyasa kuma dan kasuwa. Kafin a ba shi wannan mukami na sakataren gwamnatin Najeriya, shi ne shugaban Hukumar Kula da Rafuffukan Najeriya, (NIWA).Mista Mustapha ya kware sosai a fannin aikin gwamnati da na kamfanoni.

Haifaffen jihar Adamawa ne kuma ya yi karatunsa na sakandare a garin Hong, ya yi kwalejin kimiyya ta Maiduguri, ya yi karatun digirinsa a fannin shari'a a jami'ar Ahmadu Bello Zaria, ya kuma tafi makarantar koyon aikin shari'a a shekarar 1980 zuwa 1981.

Bayan kammala bautar kasarsa a hedikwatar rundunar sojin Najeriya, sai ya fara aiki da wani kamfanin kasar Italiya da ke Najeriya, Sotesa Nigeria Limited.

A shekarar 1983 kuma ya koma aiki da kamfanin lauyoyi na Onagoruwa & Co da ke Lagos.
Daga bisani kuma ya bude kamfaninsa na kashin kansa na aikin lauya mai suna Messrs Mustapha & Associates.

Kwarewarsa a harkar shari'a ta hada da sayar da hannayen jarin kamfanonin gwamnati.


Mista Mustapha ya taba zaman mamba na wani kwamitin gudanarwa na wucin-gadi a hukumar Tara Rarar Kudaden Man Fetur ta Najeriya, PTF, daga shekarar 2000 zuwa ta 2007.

Haka kuma ya taka rawa a shugabancin kungiyar lauyoyin Najeriya NBA, a matsayin shugaban kungiyar reshen jihar Yola.

Bayan ya bar PTF ne ya zama daya daga cikin manyan masu hannun jari na kamfanin Adroit Lex, ya kuma zama mamba na majalisar dokoki karkashin mulkin soja daga shekarar 1988-1989.

Ya shugabanci jam'iyyar PSP ta jihar Gongola a wancan lokaci a shekarar 1989-1990, da shugabancin jam'iyyar SDP daga shekarar 1990-1991.

Ya tsaya takarar gwamnan Adamawa a shekarar 1991. Ya zama mataimakin shugaban jam'iyyar ACN ta kasa daga shekarar 2010 zuwa ta 2013.

A shekarar 2007 kuma ya zama mataimakin shugaban kungiyar yakin neman zabe ta dan takarar shugaban kasar jam'iyyar ACN.

Shi ne kuma sakataren kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar APC a shekarar 2015, kuma mamba ne na kwamitin amintattu na APC.
bbchausa

No comments:

Post a Comment