Monday, 16 October 2017

Shugaba Buhari zai gana da yarinya 'yar shekaru goma dake da burin ganinshi

Wani bawan Allah me suna Hussein I. Gebi ya wallafa wata budaddiyar wasika dayace diyar dan uwanshi me shekaru gomace ta rubutata zuwa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, yarinyar me suna A'isha ta bayyana a cikintakardar tata cewa taji ance shugaba Buhari be da lafiya tana mai fatan samun sauki, kuma zataso ta ganshi gaba-da-gaba, kamar yanda ta bayyana cewa burinta shine ta hadu da shugaban kasa a zahiri, bayan Hussein ya wallafa wannan takarda ya roki jama'a su yadata domin yana so burin diyar dan uwanshi ta cika, aikuwa Allah ya amsa wannan fata nasu.Domin me baiwa shugaban kasa shawara ta fannin sabbin kafafen sadarwa Bashir Muhammad ya fito a dandalinshi na sada zumunta na shafin Twitter ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karanta wannan takarda ta A'isha kuma ya umarci da a kawota su gaisa.

Allah sark, ya Allah ka cika mana burukanmu Duniya da lahira.

No comments:

Post a Comment