Thursday, 19 October 2017

Shugaban kasa M. Buhari ya gana da takwaranshi na kasar Turkiyya Recep Erdogan

 Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a Ankara fadar gwamnatin kasar Turkiyya a tau Alhamis, Rahotanni sun nuna cewa shugabannin sun tattauna batutuwan tsaro da kuma batun 'yan cirani da sauran batutuwan da suka shafi dangantakar kasashen biyu.Shugaba Muhammadu Buhari yaje kasar Turkiyyane domin halartar taron kasashe masu tasowa da kuma yin ziyarar aiki a kasar. Muna fatan Allah ya dawo dashi lafiya.No comments:

Post a Comment