Friday, 20 October 2017

Shugaban kasa M. Buhari yayi jawabi a gurin taron kasashe masu tasowa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da jawabi a gurin taron kasashe masu tasowa dake gudana a kasar Turkiyya, bayan ya gaishe da shuwagabannin da suka halarci gurin taron shugaba Buhari ya godewa shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan bisa irin tarbar karamci da yayi mishi a lokacin daya isa kasar.Shugaba Buhari ya kuma godewa shugaba Erdogan akan irin nuna damuwa da addu'ar fatan samun lafiya daya mishi lokacin da bashi da lafiya haka kuma ya taya kasar ta Turkiyya murnar nasarar murkushe yunkurin juyin mulki da akayi a kasar, ya kuma yi fatan Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukansu a cikin wannan yanayi.
Haka kuma shugaba Buhari da shugaba Erdigan sunyi taron manema labarai a tare inda sukayi jawabai akan dangantakar kasashen biyu.

No comments:

Post a Comment