Saturday, 28 October 2017

Shugaban 'yan sanda Idris ne ya tona maganar sayawa matar shugaban kasa motoci ta hanyar almundahana dan ya tozarta ta>>Sanata Misau

Isa Hamman Misau, Sanata mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya, ya zargi Sifeta Janar na 'yan sanda wato Ibrahim Idris da fallasa takardun da su ka bayyana Aisha Buhari ta karbi kayaki da a ka samo su ta hanyar almundahana.

Misau ya ce, bayanai game da lafta-laftan motocin Jeep guda 2, da Sifeta Idris ya yarje sayawa Aisha Buhari, ya same su ne a takardun karar sa da Sifetan ya shigar a kotu.
Ya kuma ce ya yi mamakin ganin wadannan takardu cikin wadanda a ka gabatar a kotu, ganin ba su da wata alaka da shari'ar. Don haka, Misau ya ce da gangan Idris ya fallasa wadannan takardu don kawai ya tozarta mutane masu kima irin Aisha.

Misau dai ya jaddada cewan ba shi ba ne ya fallasa wadannan takardu masu dauke da sunayen mutane masu kima. A cewar sa, ya kamata ya fayyace ma mutane wannan lamari.
Naij

No comments:

Post a Comment