Friday, 27 October 2017

Shugaban ‘Yan Sandan Najeriya ya musanya kalaman Matar Shugaban Kasa


Ku na da labarin rikicin da ake yi tsakanin Sufeta Janar na ‘Yan Sanda watau IG da kuma Sanatan Kudancin Bauchi Isa Hammah Misau.

Sanata Misau ya zargi IG na ‘Yan Sanda da ba Uwargidan Shugaban kasa Hajiya Aisha Buhari kyautar wasu motoci har 2 domin hidimar ta. A cewar sa kyautar sun saba doka kuma tuni Matar Shugaban kasar ta karyata maganar.
Sai dai Sufetan yace tabbas ya ba Uwargidar Shugaba Buhari motocin ne domin kula da tsaron ta ba don hidimar kan-ta ba. Sufetan yayi wannan bayani ne ta bakin kakakin Hukumar ‘Yan Sanda Jimoh Moshood kamar yadda mu ka ji.

Hukumar ‘Yan Sanda ta ba da motocin ne ta hannun Dogarin Matar Shugaban Kasar Sani Baba-Inna. Motocin su ne Toyota Sienna da Toyota Hiace domin aiki a tawagar ta. Matar Shugaban kasar dai ba ta bayyana cewa an ba ta motocin da za su rika tsare ta ba a jiya.
naij.

No comments:

Post a Comment