Friday, 27 October 2017

Tunatarwa akan tarbiyyar yaraA wannan zamani da tarbiyya tayi karanci musamman tsakanin matasa, sare-sare, shaye-shaye, saka suturun da basu kamata ba, rashin girmama manya dadai sauran abubuwan ashsha da suka mamaye al'ummarmu, idan ka tsaya ka duba sai kaga kusan an samu nakasu ne tun daga yanda aka tarbiyyantar da yaran. Daya daga cikin hanyoyi mafi sauki da tarbiyyar yaro ke samun nakasu da kuma ba'a cika kula da itaba itace sabbin kirkire-kirkiren zamani, irin su tashoshin talabijin, wayar hannu, sai kuma abokan banza.


Idan ka kalli rayuwar yaro wallahi abin tausayice, be san me ake cewa me kyau da wanda bashi da kyau ba duk abinda aka koyamai dashi yake tashi, shiyasa suke bukatar kulawa sosai, tabbas ansan mutum bazai iyaba sai da taimakon Allah amma akwai sakaci na ganganci.

Wannan lalacewar tarbiyya ta hade gidajen masu kudi da na talakawa, talaka fitik watakila bashi da abindazai ciyar dadanshi, ya sakeshi akan titi ko kuma ya kaishi almajiranci tun baima san me ake cewa rayuwa ba, a haka yaronnan zai rika nemarwa kanshi ci dasha da sutura, zai shiga inda be kamata ya shigaba, yaga abinda be kamata ya ganiba, yaji abinda be kamata yaji ba, tarbiyarshi sai abinda Allah yayi.

Shi kuma me kudi wanda yasa 'ya 'yanshi makaranta me tsada ana kaisu a mota aje a daukosu, wasu suna baiwa 'ya 'ya waya tun kamin lokacin daya kamata su rike wayar, a barsu su kalli finafinai kala-kala, bawai sai fim din batsa bane kawai yake lalata tarbiyyar yaro ba, akwai maganganun da yaro be kamata yaji ba da wasu hotunan tashin hankali da yaro be kamata ya kallaba da kuma makirci da tuggu kala-kala da ake nuna wani marar kirki dashi a fim wanda duk yaro be kamata ya kallaba tunda shi ba iya tamtancewa zai yi ba.

Allah madaukakin sarki ya gayamana " Yaku wadanda kukayi Imani ku kare kanku da iyalanku daga wuta.....".

Haka kuma manzon Allah (S.A.W) ya gaya mana cewa "Dukkaninku makiyayane kuma za'a tambayi kowannen ku akan abinda aka bashi kiwo", 'ya 'ya suna cikin abinda za'a tambayi bawa akan yanda ya tarbiyyantar dasu Kamar yanda malamai suka gayamana.

Ta fannin abubuwan zamani na cigaba wani abin birgewa wanda yafi kowa kudi a Duniya kuma me kamfanin kwamfuta na Microsoft Bill Gates ya taba bayyana a wata hira da akayi dashi cewa be barin 'ya 'yanshi su rike waya sai sun kai shekaru goma sha hudu, yace duk da suna damunshi da ya basu amma be basu haka kuma ya kara da cewa ko kallon talabijin ya tsara musu lokutan yinshi da lokaci yayi zaice suje su kwanta dan su samu isasshen bacci, to kajifa wadanda su suka kirkiro abin kuma su Duniyarce a Gabansu.

Haka shima Steve Jobs wanda dashine aka bude shahararren kamfanin yin wayoyin da kwamfutoci na Apple ya taba bayyana cewa yana kayyadewa 'ya 'yanshi irin kayan na'urar zamani da zasu yi amfani dasu.

Kamar yanda kake kiyaye lokacin zuwa aiki da lokacin kula da kasuwancin ka da yanda kake kiyaye cin abinci idan kana jin yunwa haka kake da bukatar ko kuma ace fiye da haka kake bukatar ka kula da tar biyar 'ya 'yanka.

Allah yasa mu dace.

No comments:

Post a Comment