Monday, 23 October 2017

"Umar M. Sharif yana birgeni(ina sonshi)">>Inji Rahama Sadau

Fitacciyar jarumar finafinan Hausa Rahama Sadau ta fito ta bayyanawa Duniya cewa tana son mawaki Umar M. Sharif/ yana birgeta, Saidai abinda be fito filiba shine sone take mai na soyayya irin ta saurayi da budurwa ko kuwa soyayya a matsayinshi na abokin aikinta kuma mawaki daya iya aikinsi? dalilin dayasa baza'a iya bata fassara kaitsayeba shine saboda kalmar turancin da tayi amfani da ita ba wadda take nuna soyayyar saurayi da budurwa bace kai tsaye, zata iya nufin cewa kawai yana birgetane kuma tana son kasancewa tare dashi ko kuma tana son yin aiki tare dashi.


Umar M. Sharif dai shine ya rera wakar fim din Rahama Sadau na Raraiya wanda yanzu shine fim din da Rahamar ta taba shiryawa da kanta kuma ya samu karbuwa a cikin jama'a, yanzu haka fim din ya samu kyautar ftaccen fim na shekarar nan da muke ciki ta 2017.

Umar M. Sharif dai ya mayar mata da amsar cewa ya gode.

Rahama Sadau dai ta taba nuna alamar soyayya ga dan wasan kwallon kafa da ya fi kowane dan wasa tsada a Duniya watau Neymar, ta kuma taba rokon fitaccen dan wasan kasar Indiya Hrithik Roshan da yazo ya Aureta.

No comments:

Post a Comment