Wednesday, 18 October 2017

Wani ya kudumawa Nafisa Abdullahi zagi amma sai ta yi mai addu'a

Fitacciyar jarumar finafinan Hausa Nafisa Abdullahi tayi wani abin yabo da Jama'a da yawa suka jinjina mata akai, wanine kawai ya shiga dandalinta na sada zumunta ya aika mata da sakon zagi kamar haka "Uwaki Shegiya" , maimakon tayi fushi, ta mayarmishi da martani irin na zagin da yayi, sai Nafisa ta amsa mishi da cewa " Toh Nagode Allah ya yimaka albarka".Wannan martani data mayarmishi yasa mutane da dama sun yabeta gami da cemata ta nuna halin dattako da sanin ya kamata, kuma dama kowa irin abinda aka koyamai yakeyi.


No comments:

Post a Comment