Thursday, 5 October 2017

Wasu bayanai masu ban mamaki dangane da kudin da kake kashe kullum da baka sani ba

Image result for naira note
Kudi masu gida rana wanda a kullum rana ta Allah mutanen Duniya na ayyuka daban-daban domin su samesu, amma akwai wasu bayanai dangane da kudi wadanda baka sani ba kuma idan kaji abin zai baka mamaki amma tabbas abin haka yake, ga wasu bayanai akan kudi da zasu kara maka ilimi:


Idan kana da kudin da suka kai dalar Amurka goma ko kuma naira dubu uku da dari shida da goma sha biyar kuma babu me binka bashi. to kafi kashi ashirin da biyar na mutanen kasar Amurka arziki.

Wani bincikeya nuna cewa kashe kudi akan lamurran rayuwa da zasu karamaka ilimi da wayewa yafi kawo farinciki fiye da kashe kudin akan siyen abubuwan birgewa.

Da za'a rabawa mutanen Duniya kudin dake Duniyarnan kowane mutum zai samu Kusan Naira miliyan hudu.

Ginin dayafi kowane tsada da aka taba yi shine tashar sararin samaniya an ginata akan kudi dalar amurka biliyan dari da hamsin ko kuma ace naira tiriliyan hamsin da hudu da biliyan dari da hamsin..

A yayin da duk musulmike fatan cikawa da kalmar shahada, shikuwa shahararren mawakinnan Bob Marley daya zo mutuwa, kalmarshi ta karshe a Duniya itace "kudi basu iya sayen rayuwa".


A cikin mata guda Ashirin da sukafi kowace mace kudi a Duniya dukansu sun gaji kudinne daga kodai mazajensu da suka mutu suka bar musu gado ko kuma iyayensu maza da suka mutu suka bar musu gado, guda dayace kawai a cikinsu ba ta hanyar gado ta samu kudintaba.

Image result for pablo escobar
Wannan mutumin da ake ganin hotonshi a sama sunanshi Pablo Escobar shahararren kasurgumin dilan kwayane(Hodar Ibilis) dan kasar Kolombiyane kuma saboda yawan kudin daya tara beraye na cinye tsabar kudi dalar Amurka bilyan daya ko kuma ace Naira biliyan dari uku da sittin da daya duk shekara daga cikin kudinnashi.

Image result for bill gates
Idan da wanda yafi kowa kudi a Duniya Bill Gates zai rika kashe dalar Amurka miliyan daya ko kuma ace Naira miliyan dari uku da sittin da daya kullum rana ta Allah, to sai ya kai shekaru dari biyu da goma sha takwas kamin ya karar da kudin nashi.

A shekarun da suka gabata wasu kasashen nahiyar Afrika sun rika amfani da gishiri a matsayin kudi haka kuma kasashen China da Tibeti da Mongolia da Siberia da wasu kasashen yankin tsakiyar Asia suma sunyi amfani da ganyen shayi a matsayin kudi, kasar Siberia sai bayan da aka gama yakin Duniya na biyu sannan ta dena amfani da ganyen shayi a matsayin kudin kashewa.

A shekarun da suka gabata a bangarori da yawa na Duniya an rika amfani da dodon kodi a matsayin kudin kashewa.

Wani bincike ya bayyana cewa Kashewa wani kudinka yafi sakawa mutum farin ciki fiye da kashewa kanka.

Wani bincike da akayi ya gano cewa mafi yawancin kudin gado suna lalacewa cikin karni guda.

Wani bincike ya nuna cewa Sa'insa akan harkokin da suka shafi kudi yafi yawan kawo mace-macen aure a Duniya.

Kashi arba'in da bakwai cikin dari na mutanen kasar Amurka sun bayyana cewa idan wata matsalar kudi da yawansu yakai Naira dubu dari da arba'in ta taso musu basa iya maganinta kaitsaye ba tare da sunci bashi ba ko kuma sun sayar da wata kadararsuba.

Idan ka mutu talaka(baka da kudi) ko kuma baka da gida(matsuguni) a garin New York na kasar Amurka, to masu zaman gidan kaso/yari ne zasu binneka a cikin wani kabarin gama-gari da ake binne manyan mutane hamsin a rami daya ko kuma kananan yara dubu a rami daya.


A shekarar 2012 yawan kudin da mutane dari da sukafi kowa kudi a Duniya kedashi ya isa ya kawar da talaucin da Duniya ke fama dashi fiye da sau hudu.

Yawan kudin bashin da ake bin mutane da kamfanonin Duniya yafi yawan kudin Duniya na zahiri.

Anabin daidaikun mutanen Duniya da kamfanoni bashin kudi dalar Amurka Tiriliyan dari da casa'in da tara, amma tsabar kudin Duniya gabadayanshi da duk wasu kaya masu daraja da ake ajiyarsu a bankunan Duniya bai wuce dalar Amurka tiriyan tamanin da biliyan taraba.

Ka taba lura kuwa?: mutanen da suka mutune kadai ake saka hotunan su akan kudi.

Yawan tunanin kudi yana dauke hankalin mutum sosai ta yanda baya damuwa da bukatun da kuma matsalolin wasu.

A kididdigar kwanannan ta shekarar 2017 watan Aprilu akwai mutane biliyan bakwai da miliyan biyar a Duniya kuma me kudin Duniya watau Bill Gates zai iya ba kowane mutum na Duniya kyautar kudi Naira dubu uku da dari shida da sha biyar kuma duk da haka zai samu ragowar dalar amurka biliyan uku ko kuma sama da Naira tiriliyan daya daga cikin kudin nashi.

A shekarar 2015 shahararren kamfanin kayan sadarwa na waya da kwamfuta watau Apple yafi kasahsen Switzerland da Sweden da Najeriya kudi ko kuma ace karfin tattalin arziki.

A kasar Estonia birnin Tallin ba'a biyan kudin abin hawa, duk inda mutum zashi cikin garin kyauta za'a daukeshi.

No comments:

Post a Comment