Wednesday, 11 October 2017

Wutar Daji ta kone gidaje dubu biyu a Amurka

An samu mummunar gobarar wutar daji a kasar Amurka jihar California inda ta cinye kimanin gidaje dubu biyu, a cikin gidajen da wutar taci akwai gidajen giya da dama dana zaman mutane da guraren ayije kayayyaki, ya zuwa yanzu mutane goma sha bakwaine rahotanni sukace sunhalaka yayin da fiye da dubu dari suka bar muhallansu, rahotanni sunce wutar ta samu habakane ta hanyar cin busassun itace wanda sanadiyyar dumamar yanayi yasa suka karu, a kwanannan dai kasar ta Amurka ta hadu da bala'in ambaliyar ruwa har sau biyu. Allah shi kyauta.


No comments:

Post a Comment