Monday, 16 October 2017

Yanda ganawar shugaba Buhari da Yara uku da suka kaimai ziyara ta kasance

Burin A'isha Alitu Gebbi ya cika ayau domin kuwa ta ganana da shugaban kasa Muhammadu Buhari, a takardar data rubuta mishi tace tana daya daga cikin masoyanshi kuma tana mai fatan samun sauki haka kuma babban butinta shine ta gana dashi gaba da gaba, Nicole wadda ta baiwa shugaba Buhari kudin da ta tara sama da naira dubu biyar lokacin da yake kamfen neman zama shugaban kasa itama ta gana dashi a yau, haka kuma Maya wadda itama tayi wani bidiyo tana yiwa shugaban fatan samun lafiya tana cikin wadanda suka gaisa a yau Litinin.Shugaba Buhari ya bayyana murna da jin dadi akan irin abubuwan birgewa da yace yara ke iyayi, ya gayawa Maya cewa yaga addu'ar data yimishi lokacin bashi da lafiya kuma ya gode, haka kuma ya gayawa Nicole cewa kudin data bashi lokacin yana yakin neman zabe sun taimaka matuka domin tana iya gani yau gashi a fadar shugaban kasa kuma ya gode, haka kuma ya gayawa A'isha cewa yaji dadin takardarta daya karanta ta tabamai zuciya sosai kuma yaji dadin cewa yana da masoya har a cikin kananan yara.
Shugaba Buhari yace yana fatan wannan bazai zama lokaci na karshe da zai gana da yaraba a matsayin shugaban kasa, kuma yana fatan koda yabar kujerar shugabancin kasar zasuci gaba da ganawa da juna.No comments:

Post a Comment