Wednesday, 18 October 2017

Yanda wasu maza suka shashshafani a kofar masallacin Harami

Wannan baiwar Allahn tayi ikirarin cewa wasu maza sun tattaba mata jiki a kofar masallacin Harami dake kasa me tsarki, Makka, tace abinda ya bata mamaki shine ace gurin da yafi ko'ina tsarki a Duniya kuma tana sanye da bakin Jihabi, batayi kwalliyaba, ballantana ace taja ra'ayin mazanne amma haka suka shashsahafata.


Ta kara da cewa bayan ta wallafa wannan korafi nata a dandalinta na sada zumunta mata da yawa sun yita kiranta suna gayamata cewa suma irin wanan abin ya faru dasu.

Wani daga cikin wadanda sukayi sharhi a dandalin nata ya tambayeta anya kuwa bata ganin cewa tirmutsutsune yasa taji kamar cewa mazan suna shafata?, sai ta mayar mishi da amsar cewa ta tabbata ba tirmutsutsu bane ya shafata ne da niyya.

Sai muce Allah shi kyauta.


No comments:

Post a Comment