Monday, 16 October 2017

Yanzu haka A'isha da wasu yrara biyu dake da burin ganin shugaban kasa suna fadar shugaba Buhari dan ganawa dashi

Yarinyar da kukaji labarin ta rubutawa shugaban kasa Muhammadu Buhari wasika tana so ta ganshi watau A'isha 'yar shekaru goma da haihuwa yanzu haka tana can zaune a fadar shugaban kasar tana jiran ganawa dashi, a tare da ita a kwai wata yarinya me suna Nicole wadda lokacin da Shugaba Buhari yake kamfe din neman kujerar shugaban kasa ta bashi kyautar kidin tarar ta itama zata gana dashi a yau, yanzu shekarunta goma sha biyu da haihuwa, sai kuma Maya wadda itama diyar wata 'yar kasar wajece wadda ta taba yin wani hoton bidiyo akan shugaba Buhari.
Dukansu yau zasu gana da Shugaba Muhammadu Buhari a fadarshi, Allah ya sakawa shugaba Buhari da yayi kokarin cikawa wadannan yara burinsu.

No comments:

Post a Comment