Sunday, 29 October 2017

Yanzu zaka iya goge sakon da ka aika bisa kuskure a Whatsapp

Image result for whatsapp logo
Kana amfani da manhajar aika sako ta Whatsapp? wani lokacin idan kana catin da mutum kana aika sakon da daga baya zakaji be kamata ka aikaba? to albishirinka domin kuwa kamfanin a Whatsapp ya fito da wata sabuwar dama da ya baiwa kowane mutum idan ya aika da wani sako wanda daga baya yaji cewa akwai kuskure a sakon ko kuma yana so ya gogeshi ta yanzu zai iya yin hakan sabanin da.


Idan mutum yana so ya samu wannan dama a manhajarshi ta Whatsapp to sai ya sabuntata ko kuma ya saukar da wata sabuwar manhajar daga yanar gizo.

Amma idan mutum ya aika sako har ya wuce mintuna bakwai to bazai iya gogeshiba, watau dole ka goge sakon da kake son gogewa cikin minti bakwai da turashi.

No comments:

Post a Comment