Tuesday, 31 October 2017

Yara mata goma da suka haihu tun basu kai shekaru goma ba a Duniya

A kintacen likitoci mace tana fara nuna alamun balaga tana 'yar shekaru goma sha daya da haihuwa, daga nan jikinta zaita canjawa tana kara zama mace har zuwa shekaru sha shida zuwa shekaru sha bakwai inda a wannan lokacinne duk wata alamar balaga zata bayyana, ta zama cikakkiyar mace. Amma akwai wasu lokuta da dama da ake samun mata suna nuna alamaun balaga kuma harma su dauki ciki su haihu tun kamin sukai shekarun balaga da aka saba dasu.

Akwai yara mata da suka haihu wadanda me mafi yawancin shekaru a cikinsu itace 'yar shekara takwai me mafi karancin karancin shekaru a cikinsu itace me shekara biyar.

Gasu kamar haka:

Anna Anya, 'yar kasar Rashace, ta haihu tana 'yar shekaru takwas da wata bakwai.

Ta haihu a watan Aprilun shekarar 2000 a wani gari da ake cewa Rostov-on-Dov.
Wani yaro ne makwaucin su dan shekaru sha uku ya mata fyade bayan tayi jinin al'ada tun tana karamar yarinya kuma sai akayi sa'a ciki ys shiga.Sai kuma Hilda Trujillo, 'yar kasar Peru ce, ita ta haihu tana 'yar shekara takwas da wata bakwai.

Iyayenta talakawane da suke zaune a daki taya tal. Sun amshi bakuncin wani dan dan uwansu me shekaru ashirin da biyu, yazo ya zauna das, ashe-ashe ya lallaba ya yiwa Hilda fyade a boye ba'a saniba. Bayan faruwar abin da wata biyar sai mahaifiyarta ta lura da cikin diyarta yana girma, nan kuwa hankalinta ya tashi, ta kaita gurin likata ya dubata. Bayan likita ya duba Hilda ya tabbatarwa da mahaifiyarta tana dauke da ciki, nan kuwa aka kama wannan yaron da ya mata fyade, bayan watanni uku sai Hilda ta haifi diya mace ranar 2 ga watan Disambar 1957.
Akwai wata yarinya 'yar kasar kolombiya wadda ita ba'a bayyana sunan taba, ta haihu tana shekaru takwas da watanni biyar da haihuwa.

A shekarar 2004 mahaifiyar wannan yarinyar ta aiketa wani shagon sayar da magani ta siyomata wani magana, Ashe me shagon dan shekarun talatin da biyu da haihuwa ya mata fyade, bayan watanni takwas da faruwar lamarin sai ciki ya bayyana a jikin yarinyar, wannan yasa 'yan sanda suka kama yarinyar da mahaifiyarta bisa zargin cewa girman cikin da take dashi miyagun kwayoyine ta boye a ciki. Batan kama su ne sai suka bayyanawa jami'an tsaro cewa me kyamis dinne yawa yarinyar ciki kuma ya musu barazanar karsu sake su gayawa kowa, ranar sha daya ga watan Octoba na shekarar 2004 yarinyar ta haihu.
Akwai wata yarinya 'yar Najeriya da ake kira da Mum-Zi, itama ta haihu tana 'yar shekaru takwas da wata hudu da haihuwa.

Ita wannan yarinya ta haihu a watan disambar 1888, kuma tana cikin sa dakar wani sarki ne, da farko dai sarkin beyi niyyar tarawa da itaba domin dama a al'ada sai sadarshi tayi jinin al'ada na farko sannan yake tarawa dasu amma abin mamaki sai gashi Mum tayi jini tana 'yar karamar yarinya, sarki ya taketa kuma ta haihu, aka sawa diyar suma Zi, wani abin mamaki da wannan yarinyar shine diyar data haifa itama sai gashi ta haihu tana 'yar karamar yarinya, lokacin ta kuma tana 'yar shekaru sha bakwai da haihuwa, wannan yasa Mun-Zi ta zama kaka mafi karancin shekaru a Duniya.
Griseldina Acuna, 'yar kasar Kolombiya ce, ta haihu tana 'yar shekaru takwas da wata biyu da haihuwa.

Ita wannan yarinyar ta fara jinin al'ada tana 'yar shekaru uku kacal a Duniya kuma ta haihu ranar 13 ga watan Satumbar 1936 lokacin tana 'yar shekaru 8 da wata 2 da haihuwa.
Akwai wata yarinya 'yar kasar Indiya da ba'a bayyana sunantaba, itama ta haihu tana 'yar shekaru takwas da haihuwa.

Kasar Indiya na daya daga cikin kasashen Duniya dake fama da talauci, wannan yasa idan mutum yazo yana son yarinya koda karamace to za'a iya bashi aurenta, wannan yarinyar mahaifiyarta wadda mijinta ya mutu, ta aurawa wani mutum ita, kuma ta daiki ciki tun tana da shekaru takwas a Duniya, ta haihu a watan Agustan shekarar 1933 amma ta rasu wajan haihuwa haka jaririn nata shima ya rasu.
Sai kuma Zulma Gwadalufe Morales, 'yar kasar Meziko ce itama ta haihu tana 'yar shekaru takwas da haihuwa.

A watan Janairu na shekarar 1993 wannan yarinyar ta haihu tana da shekaru takwas, bayan watanni tara tana dauke da cikin, kawuntane ya mata ciki wannan yasa saboda kunyar abinda ya faru iyayenta suka sukayi kokarin yin komai a asirce, amma dayake maganar Duniya....., saida akaji labari.
Akwai wata yarinya itama 'yar shekara shida da wata bakwai daga kasar Indiya data haihu tana da shekaru shida da wata bakwai.

Ita wannan yarinya an bayyana ta da sunan H ne kawai domin a boye ainihin sunanta. Kuma tana shekaru shida kacal da haihuwa ta samu ciki, an kaita asibitine dalilin korafin ciwon data ce tana ji a kasan mararta,wani abin mamaki da lamarin wannan yarinyar shine lokacin data dauki cikin bata taba yin jinin al'adaba kuma mamanta basu wani girmaba, amma bayan data haihu itace ta shayar da jaririn nata har tsawon watanni tara, wannan lamari ya faru a watan Yuli na shekarar 1932.
Akwai wata yarinya me suna Yelizaveta Liza Gryshchenko yarinyar tana yankin Sobiyat ne kamin ya wargaje kuma ta haihu tana da shekaru shida da haihuwa.

Wannan yarinya tana da shekaru biyar da haihuwa a shekarun 1930 aka kaita asibiti saboda cikinta dake ta girma cikin sauri, likitoci sunyi mamakin ganin yarinyar a wannan shekaru tana da gashin gaba, kuma nonuwanta sun girma sosai idan aka kwatanta da shekarunta, sundai tabbatar da cewa tana dauke da juna biyu, kuma kakanta na wajan uwa dan shekaru sittin da tara ne ya mata wannan cikin.

Mahaifan yarinyar sunki yarda a mata aiki wajan haihuwa inda suka kafe da cewa a barta ta haihu da kanta, bayan da ta haihu jaririn bai dadeba ya rasu. Wannan abin kunya daya faru dasu yasa suka bar garin da suke saboda surutun mutane, haka kuma kakan nata da suke zaune gida daya yaci gaba da zama dasu.

Lina Medina itace uwa mafi karancin shekaru a Duniya.

Tana 'yar shekaru biyar a Duniya iyayenta suka kaita asibiti bayan da suka lura da yanda cikinta girma, a tsammaninsu wani ciwo ne take fama dashi amma da sukaje asibiti sai likita ya bayyana musu cewa yarinyar tana dauke da ciki wata bakwai, sunyi mamaki amma daga baya suka gayawa likitocin cewa yarinyar ta fara jinin al'ada tun tana 'yar watanni takwas da haihuwa haka kuma mamanta ya fara girma a lokacin data kai shekaru hudu da haihuwa.

Wannan labari ya dauki hankalin mutane sosai yanda har saida aka samu wani kamfanin yin fim na kasar Amurka suka baiwa iyayen yarinyar makudan kudi dan su bari a dauki labarin yarinyar amma iyayen basu yardaba.

Ranar 14 ga watan Mayu na shekarar 1939 Lina ta haihu bayan da likitoci suka mata aiki, a lokacin da likitocin suke mata aiki sun lura cewa duk wani abu da cikakkiyar mace take dashi itama Lina tana dashi. Bayan da ta haifi jaririn nata kuma ya fara girma, an gayamai lina yayarshice, amma da ya kai shekaru goma da haihuwa ya gane cewa mahaifiyarshice amma duk da haka sun cigaba da zama a matsayin yaya da kani.

An kama baban Lina da zargin shine ya mata ciki amma saboda babu wata kwakkwarar hujja dole aka sakeshi, ita kanta Lina bata san yanda abin ya faruba, ba zata iya cewa ga wanda ya maya cikinba, ta cigaba da rayuwa, ta kammala karatu har ta zama sakatariya a wani kamfani, amma dan nata ya mutu yana dan shekaru arba'in a Duniya.
  

No comments:

Post a Comment