Sunday, 15 October 2017

Za'a karrama fitattun jaruman finafinan Hausa a kasar Ingila

A bayar da kyautukan karramawa 'yan fim din nahiyar Afrika karo na ashirin da daya da wata jarida me suna African Voice ke shiryawa duk shekara za'a karrama jaruman finafinan Hausa na masana'antar Kannywood, bayar da kyautukan karramawar na wannan shekarar za'a yisune a birnin Landan na kasar Ingila ranar Asabar hudu ga watan Nuwamba idan Allah ya kaimu, daga cikin jaruman da za'a kartama akwai:

Nafisa Abdullahi wadda zata amshi kyautar karramawa a matsayin jaruma ta musamman/wadda tayi zarra a tsakanin jarumai mata a masana'antar finafinan Hausa.

Sai kuma Hafsat Idris wadda zata amshi kyautar karramawa ta jarumar jarumai mata ta shekara.

Sai kuma Ramadan Booth wanda zai amshi kyautar karramawa ta jarumin jarumai na shekara.Sai kuma Halima Yusuf Ibrahim wadda zata amshi kyautar fitacciyar me taimakawa babbar jaruma ta shekara.

SaiSani ahmad Yaro( shafin hutudole.com yayi kokarin gane wannan jarumi amma bamu ganoshiba) shi kuma zai amshi kyautar kartamawa a matsayin fitaccen me taimakawa babban jarumi na shekara.

Sai kuma Hamisu Lamido Iyantama wanda zai amshi kyautar karramawa ta fitaccen me shirya finafinai na shekara.

Sai kuma Kamal S.  Alkali wanda shi kuma zai amshi kyautar fitaccen me bayar da umarni na shekara(masu karrama fitattun 'yan fim na City People Award sun karrma Kamal S. Alkali da irin wannan kyauta a wannnan shekarar).

Muna tayasu murna da fatan Allah ya kara daukaka.


No comments:

Post a Comment