Monday, 6 November 2017

Yara, 'yan makarantar Firaimare sunyi zanga-zangar lumana dan nuna adawa da korar malamansu da gwamnatin jihar Kaduna ke shirin yi

A yau an samu rahotannin cewa yara 'yan makarantar firaimare a unguwar Kawo dake Kaduna sunyi zanga-zangar lumana dan nuna rashin amincewarsu da kudirin gwamnatin jihar na korar mafi yawancin malaman firaimare na jihar da suka fadi jarabawar da aka musu.Gwamnan jihar ta Kaduna Malam Nasiru El-Rufai ya dage akan cewa ba zasu yarda wadanda basu cancanta ba suci gaba da koyar da yaran da gobe sune shuwagabbnin al'ummaba, dolene a sallamesu a dauki wadanda suka cancanta.

Wannan batu dai ya jawo cece-kuce a ciki da wajan jihar ta Kaduna inda wasu ke ganin cewa ba korar  malaman ya kamata ayi ba kamata yayi a dauki nauyinsu suje su karo ilimi.

Rahotanni sun bayyana cewa akwai wani mutum da matarshi da suke aiki a makaranta daya kuma duk sunansu yana cikin wadanda za'a kora din.

No comments:

Post a Comment