Saturday, 4 November 2017

A yaune za'a karrama jaruman fina-finan Hausa a kasar Ingila; Ali Nuhu da Ramadan Booth suna can, Nafisa Abdullahi tana kan hanya

A yaune za'a bayar da kyautukan karramawa ga jaruman fina-finan Hausa a kasar Ingila wanda mujallar African Voice ta shirya bayarwa, Ali Nuhu yayi kusan sati acan kasar Ingila wanda ga dukkan alamu shine zai yiwa jaruman jagora zuwa gurin bayar da kyautukan, haka kuma shekaran jiha, wanda za'a baiwa kyautar karramawa ta jarumin jarumai watau Ramadan Booth shima ya sauka a kasar ta Ingila.Nafisa Abdullahi wadda itama za'a bata kyautar karramawa ayau din tana kan hanyar zuwa ingilar inda tabi ta kasar Faransa, Nafisar ta saka hoton wani abinci da ta tanda wanda kuma ya nuna cewa tana wani filin jirgin saman kasar Faransa inda daga canne zata karasa Ingilar.
Haka kuma Halima Atete wadda itama tana cikin wadanda za'a baiwa kyautar karramawa din tayi magana akan wannan hoton na Nafisa inda tace "yayi sai nazo"


No comments:

Post a Comment