Thursday, 23 November 2017

Abin farin ciki ya samu gwamnatin Shugaba Buhari:Kungiyar kula da harkar sufurin juragen sama ta Duniya ta gansu da ayyukan filayen Abuja da Legas a karin farko

Wani abun farin ciki ya samu a gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, kungiyar harkar jiragen sama ta kasa da kasa ce da ake kira da ICAO a takaice ta baiwa filayen jirgin saman Abuja da legas takardar gamsuwa da yanda suke gudanar da ayyukansu.

Wannan dai shine karo na farko da Najeriyar da taba samun wannan sheda a tarihi kuma a cikin kasashen yammacin Afrika najeriyarce kasa daya tilo da kungiyar ta taba baiwa wani filin jirgin samanta irin wannan sheda.

Dandalin sada zumunta na gwamnatin tarayyane ya bayyana wannan labari.

No comments:

Post a Comment